2 Satumba 2015 - 18:20

Babban sakatare janar din kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah sayyid hassan Nasrullah a lokacin ganawarsa da tawagar kasar iran da ta kai masa ziyara karkashin jagorancin mataimakin ministan harkokin wajen kasar iran Amir Abdullahiyan ya yaba game da irin rawar da kasar Iran take takawa wajen yaki da ta'adanci a yankin.

Babban sakatare Janar din kungiyar Hizbullah ta kasar labanon Sayyid Hassan Nasrullah ya jinjinawa kasar Iran game da rawar da take tawa wajen yaki da Ta’adanci.

Sayyid Nasrullah ya fadi haka ne a lokacin ganawarsa da mataimakin minsitan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin kasashen Larabawa da Afrika Amir Abdullahiyan a wata ziya da suka kai a kasar Labanon, kana ya mika sakon taya murna ga alummar kasar Iran game da babar nasarar da kasar ta samu a kulla yarjejeniya da kasashen turai kan shirinta na nakuliya na zaman lafiya da aka dake ana tattaunawa akai,

Hakazalika sayyid Nasrulla ya bayyana rawar da kasar Iran take takawa wajen yaki da ta’adanci a yanki da cewa bashi da na biyu, kana ya bukaci kasashen yankin da suka hada kai da kasar Iran wajen yakid a Ta’adanci da hare-haren masu tststsatauran ra’ayin kafrita mutane

Ana shi bangaren Amir badullahiyan ya jaddada game da muhimmancin koma teburin shawarwar tsakanin bangarorn siyasar kasar labanon da ba sa ga miciji da juna domin it ace hanya daya tilo ta tabbar da zaman lafiya a kasar kana ya zargi tsoma bakin kasashen wajen a harkokin cikin gidan a matsayin ummul habaisin kara ruruta wutar rikici a kasar.288